Kishin-kishin: ‘Yan wasan Najeriya sun fara samun sabani kafin a fara Gasan kofin Duniya

Kishin-kishin: ‘Yan wasan Najeriya sun fara samun sabani kafin a fara Gasan kofin Duniya

Mun fara samun kishin-kishin cewa baraka ta shigo tsakanin Manyan ‘Yan kwallon Najeriya na Kungiyar Super-Eagles yayin da ake shirin fara Gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa a Kasar Rasha.

Kishin-kishin: ‘Yan wasan Najeriya sun fara samun sabani kafin a fara Gasan kofin Duniya
Rikici ya shiga cikin ‘Yan wasan Najeriya Super Eagles

Rahotannin da mu ke samu daga wasu gidajen yada labarai na Kasar shi ne ana samun takaddama sosai tsakanin Kyaftin din Kungiyar kwallon na Najeriya John Mikel Obi da kuma Mataimakin sa ‘Dan wasan tsakiya watau Ogenyi Onazi.

A cikin karshen makon nan ne mu ka fara jin wannan jita-jita da babu wanda ya san gaskiyar lamarin. Ana tunanin cewa ‘Yan wasan Kasar na cigaba da yin rufa-rufa da maganar ne domin gudun a samu matsala a Gasar da za ayi kwanan nan.

KU KARANTA: Gasar World Cup: An fara sa shakka bayan Najeriya tayi wasanni a jere babu nasara

Ko da yake dai har yanzu ba mu ji takamaiman abin da ya hada manyan ‘yan wasan ba, ana cewa har ta kai ba a magana yanzu tsakanin tsohon ‘Dan wasan Chelsea watau John Mikel Obi da Mataimakin sa mai rike da kambu 'Dan wasa Ogenyi Onazi.

Sai dai wani ‘Dan wasan na Super Eagles da ya ki bari ya bayyana kan-sa ya fadawa OwnGoalNigeria cewa babu wani sabani da ake samu a Kungiyar. ‘Dan wasan ya bayyana cewa Mikel Obi wanda shi ne Shugaban ‘Yan wasan bai fada da kowa.

‘Dan wasan da ya tattauna da manema labarai yace babu wani rigima don dama can Kyaftin din na Super Eagles Mikel Obi ba mutum bane mai surutu sosai kuma yace ko da an san Onazi da hayaniya ba zai gwada yi wa Kyaftin din ba daidai ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel