FIFA: Najeriya ta sake fadowa kasa zuwa matsayi na 48 a duniya
Najeriya ta sake fado a matsayin da take a watan da ya gabata na 47 zuwa 48 a duniya, inda kuma ta kara fadowa daga na 6 zuwa na 7 a yankin Afirka, kamar yanda hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta sanar
Najeriya ta sake fado a matsayin da take a watan da ya gabata na 47 zuwa 48 a duniya, inda kuma ta kara fadowa daga na 6 zuwa na 7 a yankin Afirka, kamar yanda hukumar kwallon kafa ta duniya (FIFA) ta sanar. Hukumar kwallon kafar ta bayyana hakan ne a shafin ta na yanar gizo a jiya, inda take cewa a 'yan wasannin da Najeriya ta buga na sada zumunta shine ya jawo ta kara sauka daga matsayin nata da take a da.
DUBA WANNAN: Dandalin Kannywood: Abinda Saraki yace game da 'yan fim din Hausa
Hukumar ta sanar da cewar har yanzu wanda suke a matsayin na 1 zuwa na 3 suna nan basu canja ba, wadanda suka hada da kasar Germany, Brazil da kuma kasar Belgium, kasar Rasha, Poland da kuma kasar Uruguay sun samu nasarar fado cikin matsayi na 20.
Yayinda kasar Najeriya take a matsayin na 48, sai kuma gashi an hada ta wasa da kasashen Argentina, Croatia da Iceland wadanda suke a matsayin na 5, 20 da kuma na 22 a duniya.
A Afirka kuwa kasar Tunusiya tayi nasarar tashi daga matsayin ta 14 zuwa matsayin ta 7, inda kuma take a matsayin ta 21 a shekarun da suka gabata.
Kasar Senegal ita ce a matsayin ta 27 sai kasar Congo a matsayin ta 38, kasar Morocco ta 41 da kuma kasar Egypt a matsayin ta 45.
Kasar Ghana kuma wacce ba zata buga gasar cin kofin duniya ba, ita ce take a matsayin ta 47 a duniya, sannan kuma take a matsayin ta 6 a Afirka.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng