Alkawari kaya: Shugaba Buhari ya cika ma wani Bature alkawari bayan shekaru 22

Alkawari kaya: Shugaba Buhari ya cika ma wani Bature alkawari bayan shekaru 22

Gwamnatin Najeriya a karkashin jagorancin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta cika wani tsohon alkawari da tsohon shugaban kasa na mulkin soja, marigayi janar Sani Abacha ya daukar ma wani Baturen kasar Holland, inji rahoton Legit.ng.

A shekarar 1996 ne dai kungiyar kwallon kafa ta Najeriya ta lashe kyautar zinariya a gasar kwallon kafa na Olympic a karkashin jagorancin mai horas da kungiyar, Bonfere Jo, wannan lamari yayi ma Abacha dadi, inda ya yi alkawarin bashi kyautar gida a Abuja.

KU KARANTA: Jirgin sama dauke da mutane 10 ya yi ɓatan dabo a sararin samaniya

Alkawari kaya: Shugaba Buhari ya cika ma wani Bature alkawari bayan shekaru 22
Bonfere da yan wasan Najeriya

Haka aka yi ta tafiya har shekarar 1998, inda Abacha ya rasu ba tare da ya cika ma Jo alkawarinsa ba, gwmanatocin baya suka zo suka shude, basu cika ma wannan Baturen Alkawarinsa ba, sai a ranar Laraba, 6 ga watan Yuni Buhari ya cika wannan alkawari.

A yayin da yake mika masa makullan gidan, Ministan ayyuka, gidaje da lantarki, Babatunde Fashola ya bayyana godiyar gwamnati ga Bonfere, sa’annan ya bashi hakurin tsawon lokacin da ya kwashe yana jiran cikar wannan alkawari.

Alkawari kaya: Shugaba Buhari ya cika ma wani Bature alkawari bayan shekaru 22
Jo da Fashola

Shi ma a nasa jawabin bayan ya karbi makullan gidan ciki uku da aka gina shi a Gwagwalada, Jo ya bayyana godiyarsa ga gwamnatin Najeriya da ta cika masa wannan alkawari.

“A matsayina na wanda ya taimaka ma Najeriya wajen lashe tagulla a Olypimc da gasar cin kofin Afirka, ina yi ma Super Eagles fatan alheri a wasannin da zasu fafata na gasar cin kofin Duniya a Rasha.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng