Kalla mutumin da Real Madrid ta nada a matsayin magajin Zidane

Kalla mutumin da Real Madrid ta nada a matsayin magajin Zidane

- Kungiyar ReaL Madrid ta nada sabon Koci da zai gaji Zidane

- Julen Lopetegui ya zamo sabon mai horas da yan wasan kungiyar

Kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nada Jule Lopetegui a matsayin sabon mai horas da ita, wanda zai maye gurbin Zinadine Zidane a ranar Talata, 12 ga watan Yuni, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.

Shi dai Julen ya kasance mai horas da kungiyar kwallon kafa ta kasar Sifaniya, wanda a yanzu haka suke kasar Rasha do gwada kwanji a gasar cin kofin Duniya na shekarar 2018, don haka ake sa ran zai fara aiki a Madrid da zarar an kammala gasar.

KU KARANTA: June 12: Ba zamu lamunci soke zabe a Najeriya ba, Dan ba kara – Buhari

Kalla mutumin da Real Madrid na tana a matsayin magajin Zidane
Julen

Legit.ng ta ruwaito wata sanarwa daga Kungiyar na cewa: “Julen Lopetegui zai amshi ragamar horas da Real Madrid bayan gasar cin kofin Duniya, mun yi yarjejeniya da shi akan zai horas da kungiyar na tsawon kakan wasa guda uku.”

Tarihin Julen ya nuna ya horas da tawagr B na yan kwallon kungiyar Madrid, haka zalika ya horas da yan kwallon kasar Sifaniya yan kasa da shekaru 19, 20 da kuma yan kasa da shekaru 21, bugu da kari ya horas da kungiyar FC Porto.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel