Mutanen da ake sa ran za su maye gurbin Zidane a Madrid

Mutanen da ake sa ran za su maye gurbin Zidane a Madrid

- Kwanaki kwatsam Zidane yace ya bar Kungiyar Real Madrid

- Hakan ya zo ne jim kadan bayan ya dauki Kofin Zakarun Turai

- Ba mamaki Real Madrid ta dauko hayar Wenger ko Pochettino

Mun leka gidan kwallon kafa inda mu ka kawo maku wasu mutum 3 da ake sa ran za su maye gurbin tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane wanda a rana tsaka yace ya tashi daga Kungiyar bayan ya lashe kofin Zakarun Turai.

Mutanen da ake sa ran za su maye gurbin Zidane a Madrid
Ba mamaki Wenger ya dawo Kungiyar Real Madrid

1. Arsene Wenger

Shekaru kusan 10 da su ka wuce Real Madrid ta nemi tsohon Kocin Arsenal Wenger amma ya ki zuwa Sifen. Yanzu dai Wenger ya bar Arsenal kuma ba mamaki yana da sha’awar kwallo har yanzu don haka yana iya komawa Real Madrid.

KU KARANTA:

2. Mauricio Pochettino

Kocin Kungiyar Tottenham yana cikin wadanda ake tunani Real Madrid za su nema ya canji matsayin Zinedine Zidane. Pochettino yayi abin a zo-a gani a Ingila don haka wasu ke ganin cewa Real na iya neman sa.

3. Guti

Guti tsohon ‘Dan wasan Real Madrid ne kamar Zidane kuma yayi aiki a matsayin Mai taimakawa Kocin Kyngiyar a baya. Yanzu haka Guti yana horas da Kananan ‘Yan wasan Real Madrid kuma yana abin a yaba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng