Ashe har FIFA ta riga ta biya 'yan kwallon Najeriya kudaden su tun kafin a fara buga gasar kofin duniyan
An biya 'yan wasan Najeriya kudaden da akayi musu alkawari na buga wasan kofin duniya tun kafin a fara gasar kofin duniyan
An biya 'yan wasan Najeriya kudaden da akayi musu alkawari na buga wasan kofin duniya tun kafin a fara gasar kofin duniyan. Kamar yanda shugaban hukumar kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick, da wasu daga cikin 'yan wasan suka tabbatar.
DUBA WANNAN: Shugaba Buhari: Matasa ku cigaba da hakuri muna nan muna iya bakin kokarin mu don ganin mun dawwamar da cigaba a rayuwar ku
A watan Nuwamba ne, hukumar kwallon kafa ta Najeriya ta sa hannu akan yarjejeniya da yan wasan kwallon kafa na zata biyasu alawus da kuma wasu kudade cikin wanda aka samu na gasar kofin duniya da zasu buga a wannan shekarar.
A karkashin yarjejeniyar, za a biya yan wasan kashi 30 cikin dari na kudin da FIFA ta biya sakamakon shiga gasar da sukayi, kimanin dala miliyan 2.8.
FIFA ta fara biyan dala miliyan 2, kuma hukumar kwallon kafa ta Najeriya sun samar da dala 800,000 ta hanyar masu daukar nauyi n su.
A wasan kofin duniya na shekarar da ta gabata ne, yan wasan Najeriya suka katse horo a zagaye na 16, a wasan da zasuyi da Faransa don a biya su kudaden.
Pinnick ya sanar da majiyar mu Legit.ng cewa hukumar kwallon kafa ta Najeriya sun biya yan wasan Najeriya ne gudun abinda ya faru shekarar da ta gabata, ya maimaita kanshi.
"Mun ce zamu biyasu kafin a fara gasar kofin duniya kuma shi ne muka biyasu. Wannan abu ne mai muhimman ci a garemu domin cikin yarjejeniyar da mukayi da yan wasan, kuma mu samar musu duk abinda ya dace yanda zasu wakilci kasar mu babu damuwa."
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng