Gasar World Cup: An fara sa shakka bayan Najeriya tayi wasanni a jere babu nasara

Gasar World Cup: An fara sa shakka bayan Najeriya tayi wasanni a jere babu nasara

Masu bin harkar kwallon kafa sun fara sa alamar tambaya game da rawar da Najeriya za ta taka a kakar bana inda za a buga Gasar cin kofin Duniya a Kasar Rasha ganin yadda ake cigaba da lallasa Super Eagles a wasannin sharan-fage.

Gasar World Cup: An fara sa shakka bayan Najeriya tayi wasanni a jere babu nasara
Ana sa ran Najeriya ta tabuka abin kwarai a Gasar World Cup

A cikin ‘Yan kwanakin nan dai Super Eagles ta buga wasa da Kungiyar Atletico Madrid inda ta sha kashi da ci 2-3 a gaban Magoya bayan ta. Bayan nan ne dai Najeriya ta iya doke Kasar Folan da ci daya mai ban haushi ta hannun Victor Moses.

KU KARANTA: An kama wani sojan bogi a Najeriya

Super Eagles ta kara da Kasar Sabiya bayan ta yi wasa da Kasar Folan inda nan kuma ta dauki kashin ta a hannu. ‘Dan wasa Aleksandar Miltrovic ya jefawa Najeriya kwallaye 2 bayan an dawo hutun rabin lokaci da kuma daf da za a tashi.

Ko a wasan da Najeriya ta buga da Kasar Kongo dai kunnen doki aka tashi inda Ben Malango ya ramawa Kasar sa a minti na 78 da cin daga-kai-sai-gola. Bayan nan Najeriya ta kara shan duka a hannun Ingila a filin wasan Wembley da ci 1-2.

Wannan dai ya sa wasu su ka fara kokawa da cewa anya Najeriya za ta iya tabuka wani abin kirki a Gasan Duniya na bana inda za ta kara da irin su Kasar Argentina mai Lionel Messi da su Kasar Kuroshia. A watan nan ne dai za a fara Gasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel