Mohamed Salah ya yi barazanar barin Liverpool

Mohamed Salah ya yi barazanar barin Liverpool

Rahotanni daga kasar Spain sun ruwaito cewa fittacen dan kwallon kungiyar Liverpool Mohamed Salah ya yi barazanar barin kungiyar a nan da wani kankanin lokaci.

Taurariyar dan wasan dan asalin kasar Egypt ta haska sosai a gasar cin kofin da aka kammala a wannan kakar wasan inda gaba daya ya zuba kwallaye 44 cikin raga a dukkan wasanin da ya buga.

An dai ce Salah mai shekaru 25 ya ce zai fice daga kungiyar Liverpool ta kasar Ingila ne duk da cewa shekararsa daya katchal a kungiyar kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Mohamed Salah ya yi barazanar barin Liverpool, duba dalilinsa
Mohamed Salah ya yi barazanar barin Liverpool, duba dalilinsa

KU KARANTA: Duk da kassara magoya bayan Buhari a majalisa, an gano suna kara yawa da karfi

A cewar kafar yadda labarai ta Don Balon, ran Salah ya baci sosai ne bayan Liverpool ta janye daga cinikin siyan dan wasan kungiyar Lyon, Nabil Fekir.

Salah yana ganin Fekir zai taimaka cike wata gurbi muddin Liverpool din ta sayo shi, saidai Liverpool ta janye daga cinikin siyan tauraron kasar Faransan ne bayan ta gano ya dade yana fama da ciwon gwiwa.

Kafar yadda labarai ta Don Balon ta kara da cewa Salah ya baiwa Liverpool wa'addi zuwa karshen watan Augusta don siyo Fekir ko wani mai tsaron tsakiyar filin wasan idan ba haka ba kuma zai tafi Real Madrin ko kuma Barcelona.

Rahottani sun ce kungiyoyin na Real Madrid da Barcelona suna sahun gaba wajen neman siyyan Salah wanda ya taka muhimmiyar rawa wajen ganin cewa Liverpool ta kai wasan karshe a gasar kwararu ta Champions League.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel