Wani dan kwallon kasar Masar ya yi watsi da lambar yabo da wata kamfanin giya ta ba shi

Wani dan kwallon kasar Masar ya yi watsi da lambar yabo da wata kamfanin giya ta ba shi

Sanannen abu ne ga duk wani Musulmi cewa sha ko mu’amala da giya haramun ne a Musulunci, illa a halin da mutum babu yadda zai yi, wannan kuwa har ma wadanda ba Musulmai ba sun sani, sai dai kuma son rai yana kai wasu ga yin biris da wannan doka.

Amma da yake ba duka aka taru aka zama daya, anan an samu wani zakakurin dan kwallo da yayi kyawun kai, Mohammed El-Shenawy dake tsaron ragar kungiyar kwallon kafa ta kasar Masar, wanda a yanzu haka suke fafatawa a gasar cin kofin Duniya a kasar Rasha.

KU KARANTA: Marayu da yan gudun Hijira sun samu sabbin gidaje 200 daga hannun Dangote

Mohammed ya nuna kwazo da bajinta a wasansu da kasar Uruguay, inda ya hana kwallaye da dama shigar ragar Masar, amma daga karshe aka samu tsautsayi aka ci shi guda, wannan bajinta da ya nuna ne ya sa hukumar FIFA ta karrama shi da kyautar gwarzon dan kwallo a wannan wasa.

Wani dan kwallon kasar Masar ya yi watsi da lambar yabo da wata kamfanin giya ta ba shi
Mohammed

Sai dai dayake Muhammed na da labarin FIFA zata karrama shi ne da hadin kan wata kamfanin gida da ake kira da suna Budweiser, sai Mohammed yayi watsi da wannan kyauta, yace baya so, duk da yake ba a bukatar ya sha giya kafin a bashi, amma yace baya so, sai dai an yi kyautar ne a siffar kofin shan giya.

Ko a shekarar 2012, dan kwallon kasar Kwadebuwa, Yaya Toure ya ki amsar wata kyautar giya da ake baiwa yan kwallo bayan wasa, inda yace musu “Ni Musulmi ne, bana shan giya, don haka ku rike.”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng