Ba tsoron Allah: Labarin yadda wasu Musulmai ke karyar azuminsu don abin Duniya
Asirin wasu yan kwallon kungiyar kwallon kafa ta kasar Tunisia ya tonu bayan an bankado yadda suke dabarun karya Azumi, inda suke ganin wai sun yi wayau ne, bayan babu mahalukin da ya isa ya yi ma Allah Ubangijin talikai wayau.
Wadannan yan wasa dai a karkashin jagorancin mai tsaron ragarsu sun karya azuminsu sau dai dai har sau biyu, wanda aka gani ma kenan a idon Duniya, ba’a san na boye ba, gidan Talabijin na Aljazira ta ruwaito sun karya Azuminsu sau biyu a wasansu da kasar Portugal da kuma kasar Turkiyya.
KU KARANTA: Zakaran da Allah ya nufa da Cara: Cikakken jerin sunayen shuwagabannin APC na jihohi 36
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a yayin da ake tsaka da wasa tsakanin Tunisia da Portugarl, lokacin da ake cinsu 2-1, sai kwatsam mai tsaron ragar Tunisia, Mouez Hassen ya langabe, ya kwanta a kasa, inda nan da nan jami’an duba lafiyar yan kwallo suka garzayo wajen sa, a nan ne sauran yan kwallon Tunisian suka dauki gorar ruwa suka kwankwada.
Sai dai bayan wannan ruwa da suka sha, Zakara ta basu sa’a, inda suka mayar da biki akan kasar Portugal, suka rama kwallo daya, suka tashi da ci 2-2.
Haka zalika a karo na biyu, wasansu da kasar Turkiyya, mai tsaron ragarsu, Mouez ya kuma faduwa a minti na 49, inda yayi shame shame a kwance, anan ma sauran abokan wasan nasa sun ruga wajen tawagar yan kwallonsu, suka kwankwadi ruwa so ransu, har ma da cin dabino, bayan nan an tashi wasan kunnen doki, 2-2.
Wanna lamari na yan kwallon nan ya baiwa jama’a mamaki, ganin cewa daruruwan miliyoyin Musulmai na gudanar da Azumin Ramadana, inda suke kwashe tsawon awanni ba tare da cin abinci ko shan ruwa ba, balle kuma shan sigari ko kwanciya da iyali.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng