Alade mai nasibi da ya hango nasarar Trump a zaben Amurka, ya hangowa Najeriya nasara a gasar cin kofin Duniya
Masoya kungiyar kwallon kafa ta Najeriya sun cika da murna da farinciki bayan wani alade mai nasibi day a hango nasarar shugaba Trump gabanin zaben kasar Amurka, ya zabi kasashen Najeriya da Argentina nasarar zuwa zagayen kusa da na karshe a gasar cin kofin Duniya na kwallon kafa da za a fara bugawa a kasar Rasha.
Kazalika ya zabi kasashen Belgium da Uruguay a matsayin wasu kasashen da zasu fafata a zagayen kusa da na karshe.
Aladen da ake kira Mystic Marcus na da baiwar sansano duk inda nasara take da hancin sa kuma ya zuwa yanzu bai taba yin kuskure a hango nasara ba.
Mai Aladen, Juliette Stevens, ya bayyana cewar Aladen sa bai taba yin hasashe an samu sabani ba domin ko a gasar cin kofin duniya ta shekarar 2014 saida ya hangowa kasar Spain nasara tun kafin a fara gasar.
DUBA WANNAN: An kama wani mutum da ya shiga Ka'aba da man fetur (Bidiyo}
Wasu abubuwan ban mamaki da aladen ya yi sun hada da has ashen ficewar kasar Ingila daga kungiyar kasashen turai da kuma nasarar shugaba trump a zaben kasar Amurka, a lokacinn da jama’a tuni suka bashi faduwa.
Yanzu abin jira a gani, shine ko hancin Aladen dake sansano nasara ya sansano daidai ko akasin haka a yayin da za a fara buga gasar cin kofin Duniyar ranar juma’a a kasar Rasha.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng