Muhammadu Buhari
Mataimakiyar shugaban majalisar dinkin duniya, Amina Mohammed ta yi ta'aziyyar rasuwar shugaba Muhammadu Buhari. Ta ce Buhari ya shiga siyasa don kishin kasa.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda ya kasa jurewa yayin da yake kallon gawar tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari. Ya zubar da hawaye sosai.
Tun bayan sanar da rasuwar tsohon shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari, shugabannin duniya suka fara turo sakon ta'aziyya da alhinin wannan babban rashi.
Ana ci gaba da jimamin rasuwar tsohon shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari. Kafin Buhari akwai tsofaffin shugabanni da suka rasu tun bayan 'yancin kai.
An sada tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari da makwancinsa na karshe a cikin gidansa da ke Daura. Hakan ya kawo karshen jana'izar marigayin wanda ya rasu.
A yau Talata, 15 ga watan Yuli, 2025 za a yiwa Muhammadu Buhari sutura a birne shi a gidansa da ke Daura a jihar Katsina, ya rasu ne a ƙarshen makon da ya gabata.
Gawar tsohon shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ta iso jihar Katsina. Daga nan an wice da ita zuwa mahaifarsa ta Daura inda za a binne shi.
Filin jirgin Katsina ya cika da jama'a yayin da aka karbi gawar Muhammadu Buhari daga Landan don binne shi a Daura. Bidiyo ya nuna wadanda suka halarta.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya karɓi gawar marigayi Shugaba Muhammadu Buhari a gaban iyalansa, waɗanda idanuwansu suka cika da kwalla a Katsina.
Muhammadu Buhari
Samu kari