Muhammadu Buhari
Gwamnan Katsina, Malam Dikko Umaru Radda da tawagar kwamitin shirya jana'izar tsohon shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari sun fara tarbar manyan baƙi.
Tsohon ministan ilimi ya kare Buhari kan tallafin mai, yana mai cewa ya tsohon shugaban kasar ya ceci rayukan 'yan Najeriya daga mutuwa ta hanyar kin janye tallafi.
Tsohon mai magana da yawun shugaban ƙasa, Femi Adesina ya ce Muhammadu Buhari na zuwa neman lafiya a kasar waje tun kafin ya karɓi mulkin Najeriya.
Shugabannin kasashen duniya da suka hada da Gambiya, Chadi da Guinea Bissau za su halarci jana’izar marigayi Muhammadu Buhari a Daura jihar Katsina.
Fatima Buhari ta isa Daura cikin kuka yayin shirin jana'izar mahaifinta, yayin da gawar tsohon shugaban ke kan hanya daga Landan zuwa Katsina don binne shi.
Yayin da ake cigaba da jimamin mutuwar Muhammadu Buhari, an gano Aisha Buhari tana kuka yayin da mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ke yi mata ta'aziyya.
Ma'aikatan gidan shugaba Muhammadu Buhari sun bayyana yadda ya yi rayuwa da su a Daura bayan sauka daga mulki a 2023. Sun bayyana cewa yana kula da su sosai.
A labarin nan, za a ji cewa tuni jami'an tsaro suka cika makil a gidan tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayin da aka fara tona makwancin mamacin.
Yayin jana'izar Sarkin Ijebu da aka gudanar, sojoji sun hana yan addinin gargajiya shiga wurin sallar fitaccen basarake da aka gudanar a bisa tsarin Musulunci.
Muhammadu Buhari
Samu kari