Muhammadu Buhari
Madugun Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara jihar Katsina domin jajen rasuwar shugaba Muhammadu Buhari. Ya je gidan Buhari na Daura.
Fadar shugaban kasa ta yi martani wa ADC kan zargin siyasantar da rasuwar shugaba Muhammadu Buhari. Sunday Dare ya ce ADC ce me neman suna da rasuwar.
Tsohon ministan sadarwa, Sheikh Isa Ali Ibrahim Pantami ya yi kyautar N200,00 na rago ga Danladi Mai Kaset da ya yi wa Muhammadu Buhari takwara a Bauchi.
Ministan tsare-tsaren kasafin kudi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya fadi yadda Muhammadu Buhari ya rayu da tawali’u da gaskiya, kuma ya goyi bayan kawo sauyi.
Tsohon shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya bayyana cewa Buhari na son ministocinsa kamar yadda yake kaunar talakawa.
Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya yi magana kan rasuwar marigayi Muhammadu Buhari, inda ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah su gyara domin tsira a lahira.
Buba Galadima ya ce Alhaji Ahmadu Yaro ne babban mai taimakawa Muhammadu Buhari da kudi har ya samu nasara a 2015. Ya lissafa wadanda suka taimaki Buhari.
Tsohon Ministan sadarwa a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ta'aziyya ga wata dattijuwa da aka ce ita ta reni marigayi Muhammadu Buhari tun yana karami.
Yayin da ake cigaba da jimamin rasuwar Muhammadu Buhari, Sarkin Damaturu, Alhaji Shehu Hashimi II, ya tara manyan kasa da malamai domin addu'a gare shi.
Muhammadu Buhari
Samu kari