Jihar Benue
'Yan sanda a jihar Binuwai sun kama wasu matasa da ake zargi da kone-kone yayin zanga-zanga da aka gudanar ranar Laraba a jihar, kuma zuwa yanzu an kama mutane 18.
Wasu fisatattun matasa sun cinnawa ofishin hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) wuta a jihar Benue. Matasan dai na yin zanga-zanga ne kan matsalar tsaro.
Gwamnan jihar Benuwai, Rabaran Hyacinth Alia ya sanar da sa dokar zaman gida a ƙaramar hukumar Ukum da kewaye biyo bayan ɓarkewar zanga-zanga a yankin.
A safiyar yau ne 'yan ta'adda su ka kai hari garin Ayati a karamar hukumar Ukum inda su ka kashe mutane 11 ba haira ba dalili, wannan ja jawo mutane yin zanga-zanga.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun hallaka 'yan gudun hijira bayan sun farmake su a jihar Benue. 'Yan bindigan sun hallaka mutanen ne yayin da suke dawowa daga gona.
Jami'an rundunar 'yan sandan jihar Benue sun kai samame a wani sansanin 'yan bindiga da ke jihar. 'Yan sandan sun yi nasarar hallaka wasu tare da kwato makamai.
Al'umar karamar hukumar Ukum a jihar Binuwai sun bayyana cewa su na cikin kangin rayuwa bayan 'yan bindiga sun tilasta masu bayar da harajin wata-wata.
Rahotanni na nuni da cewa tsohon gwamna a jihar Benue na soja, AVM Adebayo Hameed Lawal (Mai ritaya) ya rasu a jiya Lahadi za a masa janaza a yau Litinin.
Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Alia, ya yi zargin cewa wasu daga cikin 'yan majalisar tarayya a jihar na adawa da shirye-shiryen ci gaba da yake da su.
Jihar Benue
Samu kari