Jihar Bauchi
Shugaban Ayyuka na Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya, Rear Admiral Musa Katagum, ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya, lamarin da ya girgiza rundunar.
Gwamna Bala ya rage awannin aikin ma'aikata a jihar Bauchi zuwa 3:00pm a Ramadan. Gwamna Abdulrazaq ya gaishe da Musulmi da Kirista yayin da aka fara azumin Ramadan.
Barista Audu Bulama Bukarti ya yi wa gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu tambayoyi game da sauke sojojin Amurka a jihar Bauchi maimakon Zamfara ko Borno.
Rundunar 'yan sandan jihar Bauchi ta kama wani mahaifi da ya daure wani dan shi tsawon shekara 17. Ya rame kamar kwarangwal, an same shi tsirara a daki.
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun kai mummunan hari gidan Limamin JIBWIS na Digare, Imam Abubakar Muhammad Digare, inda suka yi garkuwa da iyalansa.
Gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed ya halarci taron Jamhuriyar Musulunci ta Iran a Abuja. Ya yi magana kan hada kai a bangarorin noma, kiwo da fasahar zamani.
Tsohon gwamnan Bauchi, Ahmed Adamu Mu'azu ya bayyana cewa babu amfanin sabuwar gwamnatin Bauchi ta bata lokaci tana binciken Bala Mohammed idan ya sauka a mulki.
A labarin nan, za a ji cewa akwai kura a shirin da tsagin Wike na PDP ya ke yi na bude ofishin jam'iyya da aka rufe saboda rikici tsakaninsa da bangaren Turaki.
Gwamna Bala Mohammed ya sallami Kwamishinan Tsaro, Ibrahim Gambo Galadima, a yau 9 ga Fabrairu, 2026. An yi garambawul domin inganta ayyukan gwamnati a Bauchi.
Jihar Bauchi
Samu kari