Arewa
Mutane 12 sun mutu a Yar Tasha, Zamfara, bayan motar haya ta taka wani abin fashewa. An nemi gwamnati ta dauki mataki don dakatar da wannan barazanar.
Majalisar dattawa ta saurari korafin 'yan Arewa domin duba abubuwan da kudirin haraji na Bola Tinubu. Majalisar ta ce korafi ya yi yawa kan kudirin harajin.
Gwamna Ahmad Aliyu ya kaddamar da raba keken guragu 500 tare da fadada tallafin N10,000 ga mutane 10,000 domin inganta rayuwar masu bukatun musamman a Sakkwato.
Daniel Bwala ya kare kudirin harajin da Shugaba Bola Tinubu ya gabatar, yana mai cewa zai tallafawa talakawa a yankin Arewa. Ya ce mutane ba su fahimci kudurin ba.
Wasu daga cikin gwamnonin Arewa sun fara sanyi a kan kudirin haraji. Gwamna Abdullahi Sule ya ce rashin bayani ne ya haddasa adawa da kudirin daga gare su.
Mummunar gobara ta yi barna a jihohin Yobe, Kwara, da Taraba, inda ta kone shaguna da wuraren hutu tare da haddasa asarar dukiyoyi masu tarin daraja.
Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya gargadi wasu sanatoci inda ya sha alwashin tube duk wani shugaban kwamiti da ya gaza yin abin da ake tsammani.
Shugaba Bola Tinubu ya yi umarni a saurari kofare kofaren jama'a kam ƙudirin haraji da ke gaban majalisar tarayya. Ya ce ba za a cuci Arewa kan kudirin haraji ba.
Sanannen malamin addinin musulunci, Sheikh Ahmed Abubakar Gumi, ya nuna goyon bayansa kan kudirin haraji da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta kawo.
Arewa
Samu kari