Arewa
Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci hazo da ruwan sama a wasu jihohin Najeriya daga ranar Litinin, 11 zuwa Laraba 13 ga watan Nuwamba.
Tsohon hadimin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a bangaren sadarwa, Bashir Ahmad ya fadi gwamnan da ya yi fice a jihar Kano wurin kawo ayyukan cigaba.
Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Abubakar Umar Tafida da mai martaba Sarkin Argungu sun halarci jana'izar mutum 15 da aka kashe a kauyen Mera kwanan nan.
Sabuwar kungiyar Lakurawa da ta bulla a Sokoto ta fara karfi a kananan hukumomi biyar da ke jihar inda suka fara karbar Zakka daga al'ummar yankunan.
Malam Idris Abdulaziz Dutsen Tanshi ta dura kan Gwamnan Bala Mohammed na Bauchi kan take hakkin al'umma inda ya ce shi ma dan Adam ne lokacin da aka ci zarafinsa.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba zai sallami kwamishinoni da ba su tabuka komai ba domin kawo wasu sababbin jini.
An zargi jami'an NDLEA da kashe Faisal Yakubu Hussaini a Dangi, jihar Filato, yayin da suka kai samame a gidan saukar baki. Hukumar ta yi martani kan wannan zargi.
Kamfanin rarraba hasken lantarki na kasa (TCN) ya ce za a cigaba da samun matsalar rashin wuta har na tsawon lokaci kafin ya dawo yadda ya dace a kasar nan.
Gwamnatin Kaduna na shirin zuba N93 biliyan cikin shekaru hudu don gyara sashen ruwa, magance jahilcin da ya shafe shekaru goma, da inganta KADSWAC har zuwa 2027.
Arewa
Samu kari