Arewa
Fadar mai alfarma sarkin musulmi ta ba wasu matasa masu yi wa ƙasa hidima kyautar talabijin na bango watau Plasma da N100,000 bisa kyawawan halayensu.
Fitaccen mai sharhi, Reno Omokri, ya soki kisan wasu matafiya da ake zargin suna kan hanyarsu daga Port Harcourt zuwa Kano don hutun bukukuwan Sallah.
Wasu mutanen Arewa da suka fito daga Fatakwal zuwa Kano sun hadu da tsautsayi a jihar Edo. An kona yan Arewa 16 a Edo suna dawowa gida hutun sallar azumi.
Sarki Muhammadu Sanusi II ya fitar da sanarwa kan yadda bikin zai gudana a Kano bayan Sarki na 15, Aminu Ado Bayero ya janye daga hawan saboda dalilan tsaro.
Fashewar tankunan mai a Jihar Neja sun hallaka akalla mutane 112 tare da lalata kadarorin da darajarsu ta kai biliyoyin naira tsakanin Janairu da Maris 2025.
Gwamnan Plateau, Caleb Mutfwang ya kulla yarjejeniya da Isra'ila kan aikin noma, fasaha da kiwon lafiya domin bunkasa tattalin arziki da inganta rayuwar al’umma.
Yayin da ake shirin yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kiranye, INEC ta gudanar da taro kan lamarin bayan fiye da masu zabe 250,000 sun sa hannu kan bukatar hakan.
Gwamna Muhammadu inuwa Yahaya ya nada Baffan sarki, Alhaji Bappah Ibrahim Mohammed a matsayin sabon Hakimin Masarautar Gombe, mataimakin gwamna ya kai masa takarda.
Gwamna Alia na jihar Benuwai ya yi fatali da masu kiraye-kirayen a ayyana dojar ta ɓaci kamar yadda aka yi a jihar Ribas saboda abubuwan da ke faruwa.
Arewa
Samu kari