Arewa
Rahotanni sun ce ‘yan sanda sun tabbatar da kwace adduna biyu daga wurin da lamarin ya faru, sannan an mika bincike ga sashen CID domin gudanar da cikakken bincike.
Bayan rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi, Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero, ya soke duk wasu shirye-shiryen bukukuwan sallah da aka tsara.
Dan sanda a Kaduna mai suna Hadaina Hussaini Dan-Taki ya jawo kansa matsala da ya yi barazanar daukar mataki kan ‘yan Kudu da ke Arewa bayan kashe wasu a Edo
Mazauna garin Uromi a karamar hukumar Esan ta Arewa maso Gabas sun fara zama a cikin zullumi saboda fargabar harin ramuwar gayya kan kisan Hausawa.
Ciyaman din Okehi da ke jihar Kogi ya sanya dokar hana fita a fadin karamar hukumar, saboda barazanar tsaro. An dauki matakin ne gabanin zuwan Sanata Natasha.
Gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam na kasa da kasa, reshen Najeriya, Kwamred AA Ayagi ya bayyana cewa ba za su tsuke bakinsu a kan kisan Hausawa a Edo ba.
Shugaban hadaddiyar kungiyoyin masu fataucin dabbobi da kayan abinci ta kasa, Dr. Muhammad Tahir ya bayyana yadda aka hango matsala ga 'yan kasuwar Arewa a Kudu.
'Yan sanda sun musanta jita-jitar da ake yadawa kan kai wa Inyamurai Igbo hari a Kano, sun fara bincike don kama wadanda ke yada karyar, tare da yin babban gargadi.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya karbi bakuncin takwaransa na Edo, Sanata Monday Okpebholo bayan kisan Hausawa.inda ya raka shi yiwa iyalansu jaje.
Arewa
Samu kari