Arewa
Rundunar ƴan sanda a jihar Taraba ta cafke wasu jami’an hukumar zaɓe mai zaman kanta ta kasa (INEC) tare da kwato kayayyakin zaɓe da ake zargin sun karkatar.
Yayin da za a shafe kwanaki 3 ana sheka ruwan sama a Arewacin Najeriya, NiMet ta ce za a samu ambaliya a Kebbi, Gombe da Bauchi da wasu jihohin Arewa ta Tsakiya.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa jihar Kebbi ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru da ke jihar a Arewa maso Yamma a Najeriya.
Jam'iyyar PDP reshen jihar Kaduna ta bayyana kudin da aka kwace daga hannun wakilinta ba na sayen kuri'u ba ne, kudin gudanar da harkokin zabe ne.
Mun samu labarin rasuwar shahararren ɗan kasuwa kuma dattijon Arewa, Alhaji Isiaku Ibrahim a yau Asabar wanda ya rasu a asibitin Abuja yana da shekara 88.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa wasu yan bindiga sun sace Alhaji Adamu, mai taimaka wa tsohon gwamna Tanko Almakura, daga gidansa a birnin Lafia.
Majalisar wakilai ta yi barazanar hukunta mabanta Ibrahim Auyo idan bai kawo hujja kan zargin cewa ana biyan kuɗi kafin gabatar da kudiri ko ƙudirin ƙuduri.
Hukumar NiMet ta yi gargadin ambaliyar ruwa a jihohin Kebbi da Neja a ranar Asabar. Hukumar ta shawarci mazauna jihohin su dauki matakan kare kansu da dukiyoyinsu.
Rundunar yan sanda ta bayyana cewa daga karfe 12:00 na dare mai zuwa, ta haramta zirga zirga a kananan hukumomi hudu da za a gudanar da zaben cike gurbi a Kaduna.
Arewa
Samu kari