Arewa
Fitaccen mai barkwancin nan daga Arewa, Umar Bush ya samu mukamin mai tallafawa Hon. Mohammed Abba Isah kan harkokin nishadi a ofishin Shugaba Bola Tinubu.
Majalisar jihar Kano ta gabatar da kudirin samar da sarakuna guda uku masu girman daraja ta biyu da za su ƙasa ƙarƙashin Sarki Muhammadu Sanusi II.
Sarkin Dawaki Babba, Baffa Dan Agundi ya bayyana kuskuren da aka yi tun farko kan mayar da Sanusi II sarauta inda ya ce shi ba ɗan sarki ba ne domin gadonta ake yi.
Bayan yanke hukunci kan dambarwar sarauta, Kungiyar Kano Democratic Vanguard ta ce hukuncin abin kunya ne ga bangaren shari'a ganin yadda aka nuna son kai a fili.
Kungiyar matasan Arewa ta Arewa Youth Ambassadors (AYA) to kori shugabanta, Yahaya Abdullahi, inda ta zarge shi da son rai da kabilanci.l, tare neman a yi bincike.
Ruwan sama mai karfi ya ruguza gidaje da dama a kamar hukumar Michika a jihar Adamawa. Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri ya yi alkawarin kai musu tallafi.
Manyan malaman addinin Musulunci a Arewacin Najeriya sun rabu gida biyu kan ko ya halasta a fita zanga-zanga saboda tsananin rayuwa da ake fama a kasar.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nada dan tsohon gwamnan jihar Kwara, Cornelius Oluwasegun Adebayo a matsayin shugaban hukumar NALDA da ke kula da harkokin noma.
Ana fargabar gobara ta jawo asara mai tarin yawa a fadar Sarkin Kano bayan iftila'in da ya faru a daren jiya Juma'a 12 ga watan Yuli 2024 a fadar da ke Kofar Kudu.
Arewa
Samu kari