Arewa
Rahotanni sun nuna wani mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahiraa jihar Jigawa kan zarginsa na ɗaukar burodi, madara da indomi, yan sanda sun kama shi.
Sarkin Katstina ya yi babban rashi yayin da kaninsa Hassan Kabir Usman ya rasu. Gwamna Dikko Umaru Radda ya tura sakon jaje ga masarautar katsina kan rashin.
Hukumar NiMET ta gargadi mazauna wasu jihohi shida na Arewacin Najeriya da su shirya ganin ruwan sama mai hade da tsawa da iska mai karfi a kwanaki masu zuwa.
Gwamnatin tarayya ta ce mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya kashe akalla mutane 49 a jihohin Taraba, Adamawa da Jigawa,ana fargabar karuwar ambaliya.
Ana zargin hakimin da ke kula da wasu yankuna a jihar Kano wanda Sarki Sanusi II ya nada shi ya sallami dagatai guda uku daga sarauta da ake ganin ya saba ka'ida.
A ranar 26 ga watan Agusta ake murnar ranar Hausa a duniya. Legit Hausa ta tattaro muku hukuncin ranar Hausa a Musulunci, muhimmancin koyon ka'idojin rubutun Hausa
Kwamishinan kudi na jihar Borno, Ahmed Ali Ahmed ya kwanta dama. An ce ya rasu ne a safiyar yau Litinin, 26 ga Agustan 2024 a cikin gidansa da ke Maiduguri.
Wasu yan bindiga sun sace hakimin Garu Kurama, Yakubu Jadi da wasu mutane shida a kauyen Gurzan Kurama da ke Kaduna ta Kudu a daren ranar Juma'a da ta gabata.
Sanata Aminu Waziri Tambuwal ya kaɗu bayan rashin da ya tafka na kaninsa, Alhaji Ahmad Ibrahim Tambuwal a jiya Asabar 24 ga watan Agustan 2024 a birnin Abuja.
Arewa
Samu kari