Arewa
Sanatan Kaduna ta Tsakiya, Lawal Adamu ya soki kungiyar da ta yi barazanar masa kiranye inda ya ce ba zai bata lokacin wurin fahimtar da su ayyukan da yake yi ba.
Za a ji cewa Gwamnan jihar Kaduna, Uba Sani ya mika sakon godiya ga Bola Tinubu kan samar da hukumar cigaban Arewa ta yamma (NWDC) domin farfado da yankin.
Gwamna Nasir Idris na jihar Kebbi ya kori dukkan shugabannin riko na kananan hukumomi 21 a jihar yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zabe a watan Agustan 2024.
Shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya sanya hannu kan kudurin dokar samar da hukumar raya yankin Arewa maso Yamma. NWDC ita ce irinta ta uku a Najeriya.
Cibiyar kididdiga ta NBS ta fitar da rahoto kan jihohi da yankuna da aka fi tsadar kayan abinci a Najeriya. Abia, Legas, Abuja, Gombe suna cikin jihoh masu tsada.
Hafsun sojojin Najeriya, Laftanal Janar Taoreed Lagbaja ya bayyana hakar ma'adanai da satar shanu cikin manyan abubuwan da ke kawo cikas wajen yakar yan ta'adda.
Gwamnatin jihar Zamfara ta yi martani ga Bello Matawalle inda ta tabbatar da cewa babu abin da zai saka ta zaman tattaunawa da 'yan bindiga saboda ba mafita ba ne.
Kungiyar matasan Arewa ta janye shirinta na zanga-zanga inda ta ce akwai lauje cikin nadi daga Kudancin Najeriya domin kawo rigima a Arewacin Najeriya.
Jami'ai da ake zargin na farin kaya ne sun cafke wani Bashir Yunusa bayan ya tallata rigar zanga-zangar da ake shiryawa a Najeriya kan yunwa da matsin rayuwa.
Arewa
Samu kari