Arewa
Kamfanin rarraba wuta na ƙasa TCN ya tabbatar da cewa wasu mahara sun tafka ɓarna a tashar wutar da ake ginawa a Obajana da ke jihar Kogi a Arewa ta Tsakiya.
Gwamnatin Kano karƙashin Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ta karyata raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta ciyo bashin N177bn daga wani mai bada lamuni a Faransa.
Hadimin shugaban karamar hukumar Tangaza a jihar Sokoto, Gazali Aliyu ya fadi irin ta'addancin da Lakurawa ke yi tare da sauya limamai a masallatai.
A yayin da ake kuka cewa 'yan ta'addar Lakurawa sun fara karfi, gwamnan Sokoto, Ahmad Aliyu ya gana da ministan kudi, Mista Wale Edun kan ci gaban tattalin jihar.
Hukumar EFCC ta yi bincike kan bidiyon cin zarafin naira a wani biki a Kano, inda aka zargi Fauziya Goje, amma bincike ya tabbatar da cewa ba ta da alhakin hakan.
Kungiyar Arewa Consensus for Jonathan (ACJ) ta bayyana nadamar kin zaben Jonathan a 2015, tana yabawa da irin ci gaban da ya kawo yankin Arewa a fannin ilimi.
Shugaban majalisar wakilai, Rt Hon. Tajudeen Abbas ya bayyana cewa galibin ƴam Najeriya ba su fahimci nauyin da ƙe kan ƴan majalisa a tsarin demokuraɗiyya ba.
Gwamnan Benuwai, Hyacinth Alia ya sanar da maido da antoni janar kuma kwamishinan shari'a kan kujerarsa bayan ya cika haruddan da aka gindaya masa.
Hukumar NiMet ta yi hasashen cewa za a fuskanci hazo da ruwan sama a wasu jihohin Najeriya daga ranar Litinin, 11 zuwa Laraba 13 ga watan Nuwamba.
Arewa
Samu kari