Abun Bakin Ciki
Atiku Abubakar ya jajanta wa iyalai kan turmutsitsin da ya yi ajalin rayukan mutane a jihohin Najeriya, ya bukaci matakan tsaro don kare faruwar irin hakan a gaba.
Turmutsitsin Anambra ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 22. Wadanda suka samu raunuka suna kwance a asibiti yayin da ake bincike kan yadda hakan ta faru.
Hankulan mutane sun tashi yayin da wani iftila'i da ya faru a jihar Ondo da yammacin yau Asabar bayan faduwar tankar man fetur da ya yi sanadin konewarta kurmus.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya nuna takaici bayan aukuwar iftila'in da ya yi sanadin mutuwar mutane a Abuja da Anambra inda ya fasa gudanar da bukukuwan ya shirya.
Mutum 27 sun mutu a turereniya yayin rabon shinkafa a Okija, Anambra. Ganau sun bayyana yadda kyakkyawan niyya ya koma masifa, bayan mutane sun rasa rayuka.
Rundunar ƴan sanda ta tabatar da nutuwar ɗaliban Jami'ar OOU 3 a wani mummunan hatsarin mota da ya afku jiya Juma'a, wasu mutum 2 na kwance a asibiti.
Wasu majiyoyi sun tabbatar da mutuwar yara bakwai da wasu mutane uku yayin turereniya domin samun kayan tallafi saboda halin kunci a wani coci a Abuja.
Kotun Abuja ta tsare Olamide Thomas kan tuhume-tuhume uku da suka shafi barazana ga dan shugaban kasa. An dage shari’ar zuwa 30 ga Disamba don ci gaba.
Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Oyo sun nuna cewa an tafka asarar makudan kuɗi a gobarar da ta tashi a kasuwar sayar da kayan gayarn ababen hawa.
Abun Bakin Ciki
Samu kari