Abun Bakin Ciki
Tsohon kwamishinan yaɗa labarai da sadarwa na jihar Kwara, Alhaji Abdulrahim Adisa ya kwanta dama, ya rasu yana da shekaru 91 a duniya ranar Alhamis.
Soja ya kashe matashi Abdullahi Muhammad a kofar barikin Rukuba. Rundunar sojoji ta fara gudanar da bincike, tare da yin alkawarin adalci da hukunta mai laifin.
Hukumomi a Karamar Hukumar Garun Malam a jihar Kano sun rufe Kasuwar Tumatur ta Kwanar Gafan saboda zargin ayyukan fasadi, karuwanci da wasu munanan dabi'u.
Matar tsohon gwamnan Ondo, Betty Akeredolu ta yi kaca-kaca da Gwamna Lucky Aiyedatiwa kan shirin gudanar da taron tunawa da mijinta, Rotimi Akeredolu.
Masu garkuwa da mutane sun kashe wani yaro dan shekara 10 Tasi’u Abdullahi a Filato duk da karbar kudin fansa. An rahoto cewa an gano gawarsa ne a cikin buhu.
Barayi sun haura katanga, sun sace akuyar Kirsimet a Gwagwalada da ke Abuja. Mai akuyar ya kai rahoto yayin da ‘yan sanda suka soma bincike don gano barayin akuyar.
Hukumar kiyaye haɗurra ta ƙasa FRSC ta tabbatar da mutuwar mutum uku, wasu huɗu sun jikkata a wani hatsarin da ya rutsa da ɗan adaidaita sahu a jihar Jos.
Jirgin kasa ya murkushe mota dauke da buhunan shinkafa a yankin Iju-Fagba, jihar Legas. Jama’a sun koka kan rashin shingen tsaro da alamar isowar jirgi.
Tsohon mataimakin sufetan rundunar ƴan sanda na ƙasa, Bola Longe ya riga mu gidan gaskiya, ya rasu ne ranar Lahadi da ta gabata bayan fama da jinya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari