Abun Bakin Ciki
Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde ya miƙa sakon ta'aziyya ga iyalai da ƴan uwan tsohon shugaban hukumar OYSAA kuma babban jigon PDP, Hon. Temilola Segun Adibi.
Rahotanni sun nuna cewa ɗan kwamishinan ƴan sandan Abuja, Olatunji Disuya mutu a wani hatsarin mota da ya rutsa da shi ranar Litinin, 20 ga watan Janairu, 2025.
Wani jami'in dan sanda, Lawal Ibrahim da ke aiki a sashen rundunar na Kwali, ya rasu a otel ɗin Gwagwalada bayan gama jima'i da wata budurwa, Maryam Abba.
An rasa fasinjoji 3 daga cikin 22 a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a yankin ƙaramar hukumar Bonny a jihar Ribas, yan sanda sun tabbatar da ceto mutum 19.
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya miƙa sakon jaje da ta'aziyya ga gwamnatin Neja da al'ummar jihar bisa fashewar tankar da ya jawo asarar rayuka.
An gudanar da jana'izar mutum 86 daga cikin wadanda suka mutu a gobarar tankar man fetur a jihar Neja yayin da wasu 'yan kasuwa suka rasa dukiyoyinsu.
Allah ya karbi rayuwar mahaifiyar jarumi Yaya Ɗanƙwambo, an yi mata sutura a Samarun Zaria. Haka zalika, Mahaifin jarumi Baba Ari ya rasu, kuma an yi masa sutura.
Hukumomi a jihar Niger da ke Arewacin Najeriya sun tabbatar da cewa yawan mutane da suka mutu sanadin hatsarin tankar fetur sun kai 86 yayin 55 suka samu raunuka.
Rahotanni sun tabbatar da cewa uwargidan tsohon gwamnan farko na jihar Delta, Olorogun Felix Ibru ta riga mu gidan gaskiya a birnin London da ke Burtaniya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari