Abun Bakin Ciki
Bayan zargin cin zarafi da wani basarake ya yi, Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Oba Abdulsemiu Ogunjobi na Orile Ifo na tsawon watanni shida daga sarauta.
Rikici ya barke a garin Esa-Oke bayan nadin sabon sarki, inda wasu suka kai farmaki da kashe mutane da dama. ‘Yan sanda sun ce ana kokarin shawo kan lamarin.
Gwamnatin Ogun ta fara bincike kan bidiyon da ya nuna Oba Ogunjobi yana cin zarafin Cif Arinola, yana la’antar shi da barazanar amfani da ‘yan sanda kansa.
An sake samun wani sabon bidiyo da ya nuna Kachallah Bugaje wanda ya koma Zakiru yana jagorantar addu’a tare da yaransa, bayan da ya ce ya daina ta’addanci.
Jami’an NDLEA sun kama dan kasuwa, Chijioke Igbokwe da hodar Iblis 81 a cikinsa. An yi masa tiyata bayan da ƙwayoyi 57 sun makale masa bayan kwanaki bakwai.
Gwamnatin Osun ta ce ta shirya daukaka kara bayan hukuncin kotu, inda ta bukaci a zauna lafiya har sai kotun daukaka kara ta yanke hukunci kan rigimar sarauta.
Dan daudu, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya bayyana yadda ya rasa budurcinsa kuma ya dirka wa wata mace juna biyu lokacin da yake jami’a.
Gwamna Caleb Mutfwang na Plateau ya sallami kwamishinoni biyar daga majalisar zartarwa, inda aka nada sababbi domin maye gurbinsu ba tare da bata lokaci ba.
Jirgin Max Air dauke da fasinjoji 59 ya yi hatsari a jihar Kano. Tayar jirgin ta fashe tare da kamawa da wuta, amma jami’ai sun yi gaggawar kwace mutanen.
Abun Bakin Ciki
Samu kari