Mutane Sun Bar Kasuwancinsu da Noma Baki Daya domin Alhinin Tsohon Gwamna
- Al’ummar masarautar Umeh da ke Delta za su dakatar da kasuwanci, noma da bukukuwa ranar Juma’a domin jimami
- Mai jiran gadon sarautar Umeh, Meshack Owhe, ya ce za su ƙara ranar jimamin da gwamnati ta ayyana
- Al’ummar sun yaba wa marigayi Emmanuel Uduaghan bisa gina musu hanyar Umeh, gyaran makarantar firamare
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Umeh, Delta - Mai jiran gadon sarautar masarautar Umeh da ke ƙaramar hukumar Isoko ta Kudu a jihar Delta, Meshack Owhe, ya ayyana ranar hutu domin yin makoki.
Basaraken ya ayyana ranar Juma’a, 23 ga Oktobar 2026, a matsayin ranar jimami domin girmama marigayi tsohon gwamnan jihar Delta, Dakta Emmanuel Uduaghan.

Source: Facebook
An sanar da makoki bayan mutuwar Uduaghan
Sarkin, yayin sanar da matakin a ranar Laraba cikin saƙon ta’aziyya a madadin al’ummar Umeh, cewar Punch.
Ya bayyana tsohon gwamnan a matsayin mai kishin ƙasa, fitaccen ɗan Delta kuma ɗaya daga cikin manyan ’ya’yan al’ummar Itsekiri, wanda gudummawarsa za ta ci gaba da kasancewa abin tunawa a jihar Delta da sauran wurare.
Basaraken ya ce:
“Al’ummar za su dakatar da kasuwanci, noma da dukkan bukukuwa tun daga wayewar gari har zuwa faduwar rana, domin girmama gudummawar da Uduaghan ya bayar wajen ci gaban al’ummarmu.”
Mai jiran gadon sarautar ya tabbatar da cewa masarautar za ta bi umarnin kwanaki uku na jimami da gwamnatin jihar Delta ta ayyana daga ranar 19 ga Oktoba, inda za a saukar da tutoci zuwa rabin mast. Sai dai al’ummar Umeh za su tsawaita nasu jimamin har zuwa ranar Juma’a.
Ya lura cewa rasuwar Uduaghan ta kawo ƙarshen wani muhimmin zamani a jihar Delta, yankin Kudu maso Kudu da Najeriya baki ɗaya.
Ya tuna da shekarun da marigayin ya yi yana aiki a matsayin likita, kwamishinan lafiya, sakataren gwamnatin jiha da kuma gwamnan Delta na wa’adi biyu daga 2007 zuwa 2015.
A cewar mai jiran gadon sarautar, al’ummar Umeh za su ci gaba da godiya bisa ayyukan ci gaba da tsohon gwamnan ya samar musu da kuma kyakkyawar alaƙar da ya ƙulla da al’ummar.
Ya tuna da alaƙa ta musamman da Emmanuel Uduaghan ya yi da masarautar Umeh, inda ya ce ziyarar da tsohon gwamnan ya kai al’ummar ranar 24 ga Agusta, 2011, bayan wani gangamin neman gina hanyar Umeh ta zama wani muhimmin sauyi a tarihin al’ummar.
Ya ce:
“A lokacin, Umeh al’umma ce ta noma wadda ba ta samu ci gaba sosai ba, kuma ta shafe shekaru ba tare da hanya ba, duk da roƙon da aka yi wa gwamnatoci daban-daban tun daga tsohuwar jihar Bendel.”
An dawo da gawar tsohon gwamna Delta
Mun kawo muku cewa Gwamnan Delta, Sheriff Oborevwori, ya karɓi gawar tsohon gwamnan jihar, Emmanuel Uduaghan, a filin jirgin saman Osubi.
Peter Obi, Godwin Obaseki da sauran manyan ’yan siyasa sun yi alhinin rasuwar Uduaghan, tare da yabawa gudummawar da ya bayar wajen ci gaban Delta.
Masu jimamin rasuwar Uduaghan sun bayyana shi a matsayin jagoran da ya haɗa kan al’umma, ya inganta zaman lafiya, lafiya, ilimi da ababen more rayuwa.
Asali: Legit.ng

