Abun Bakin Ciki
Rundunar 'yan sanda ta kama wani Gbolahan Adebayo bisa zargin kashe budurwarsa da duka a Legas. An dauki gawarta zuwa asibiti domin gudanar da bincike.
Jihar Benue ta sanar da barkewar zazzabin Lassa, inda mutum 5 suka kamu, 3 sun mutu. Gwamnati ta dauki matakan dakile cutar tare da wayar da kan jama’a.
Rahotanni sun tabbatar da mutuwar dan kwallon Najeriya, Abubakar Lawal, wanda aka ce ya fado daga bene na uku a birnin Kampala da ke kasar Uganda.
Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Edo a inuwar jam'iyyar LP, Olumide zakpata ya sanar da rasuwar mahifinsa da kuma kawunsa, ya ce rashinsu ya jijjiga shi.
Rikicin kabilanci tsakanin mazauna garuruwan Gbelemonti da Maidoti a jihar Edo ya jawo mutuwar mutane 7, tare da jikkata 6. ‘Yan sanda da sojoji sun dakile lamarin.
An yada wani faifan bidiyo da aka gano marigayi Sanata Lawal Yahaya Gumau yana fadin ya kusa mutuwa makwanni kafin sanar da rasuwarsa a jiya Asabar.
Rahotanni sun tabbatar da cewa tsohon sanatan Bauchi ta Kudu, Lawal Yahaya Gumau, ya rasu a Abuja bayan gajeriyar rashin lafiya inda aka shirya yi masa jana'izarsa.
Al'ummar Remo da Gwamnatin Ogun sun shiga jimami bisa rasuwar Oba Idowu Basibo, wanda ya shafe shekaru 22 yana mulkin Iperu, Bola Tinubu ya jajanta musu.
Tsohon shugaban kasa a mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida mai ritaya ya tona yadda marigayi Janar Sani Abacha ya shirya kisan MKO Abiola.
Abun Bakin Ciki
Samu kari