Abun Bakin Ciki
Sanata Geraldine Thompson ta jihar Florida a ƙasar Amurka ta riga mu gidan gaskiya bayan an mata tiyata domin gyara mata gwiwarta a ƙasar Amurka.
‘Yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu a Gwargwada, Abuja, saboda jinkirin fansa. Sun sako wasu mutum uku bayan karɓar N3m. Har yanzu ba a samu gawarwakin ba.
Wasu rahotanni sun ce ana hasashen batan tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi, Umar Namashaya Diggi bayan wani mummunan harin yan bindiga.
Jami'ar Tarayya da ke Lokoja a jihar Kogi ta bayyana alhininta bisa mutuwar ɗalibanta biyar a wani mummunan hatsarin mota da ya rutsa da su, ta dakatar da karatu.
Kungiyar gwamnonin Najeriya watau NGF ta bayyana alhininta bisa rasuwar jagoran PANDEF, Edwin Clark da jagoran Afenifere, Ayo Adebanjo, ta ce kasa ta yi rashi.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Tinubu ya jajanta bayan rasuwar shugaba a kungiyar PANDEF, Cif Edwin Clark a yau Talata inda ya ce an yi rashin kishin kasa.
FBI ta cafke Oba Joseph Oloyede, Sarkin Ipetumodu, bisa zargin satar kudaden tallafin COVID-19. Ya samu miliyoyin daloli ta hanyar takardun karya.
Rikicin siyasa a Osun ya yi sanadiyar mutuwar mutum 6. Rundunar 'yan sanda ta tura karin jami’an tsaro don kwantar da tarzoma tare da hukunta masu haddasa rikicin.
Masu garkuwa da mutane, dauke da muggan makamai sun farmaki gidan wani faston cocin RCCG. An ce 'yan bindigar sun kashe dan faston tare da sace matarsa.
Abun Bakin Ciki
Samu kari