Abun Bakin Ciki
A tsakanin Janairu zuwa karshen Maris din 2025, Najeriya ta yi rashin wasu fitattun 'yan siyasa biyar, ciki har da Chief Edwin Kiagbodo Clark, Adewunmi Onanuga.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya karbi bakuncin takwaransa na Edo, Sanata Monday Okpebholo bayan kisan Hausawa.inda ya raka shi yiwa iyalansu jaje.
Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo ya kawo ziyara ta musamman ga Abba Kabir Yusuf domin jajanta masa kan kisan gilla da aka yi wa Hausawa a garin Uromi.
Rundunar ‘yan sandan Katsina ta cafke wani mutum, Alhaji Surajo Mai Asharalle da wasu uku kan zarginsu da kai wa jami’an Hisbah hari, inda suka jikkata su.
Bayan kisan ƴan Arewa a jihar Edo, babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya yi Allah wadai da kisan gilla da aka yi wa wasu mafarauta.
Bayan kisan wasu ƴan Arewa fiye da 16 a Uromi da ke jihar Edo, a yau Asabar 29 ga watan Maris aka birne wasu daga cikinsu bayan samun gawarwakinsu.
Bayan Peter Obi ya jajanta kan kisan wasu ƴan Arewa a Edo, an taso shi a gaba kan yadda ya yi jajen tare da neman a hukunta masu kisan ƴan jihar.
Shugaban Kungiyar Izalah a Najeriya, Sheikh Abdullahi Bala Lau ya nuna bakin cikinsa kan kisan matafiya a jihar Edo, ya yi kira ga hukumomi da su bincika.
‘Yan bindiga sun kashe mutane 10 a Ruwi, Bokkos. Rundunar ‘yan sanda ta tura jami’ai, yayin da gwamnatin Filato ke kokarin kawo karshen hare-haren.
Abun Bakin Ciki
Samu kari