Abun Bakin Ciki
Wani fasto a Ibagwa-Aka, Igbo-Eze ta Kudu da ke jihar Enugu, ya halaka yara hudu da tabarya lamarin ya girgiza al’umma tare da tayar da hankulan mutane.
An kuma asarar rayuka bayan wani hatsarin jirgin ruwa ya halaka mutum 27 a Gbajibo, karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, yayin dawowa daga kasuwa a Niger.
Gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno ya fusata yadda wasu kwamishinoni da sauran hadimansa ke watse masa a filin taro inda ya ce wannan rashin da'a ne.
Hukumar Hisbah ta jihar Yobe tare da hadin guiwar hukumomin NDLEA da NSCDC sun rufe 'Maina Lodge' a birnin Damaturu, inda suka kama katon 209 na giya.
Ya sanda a Jihar Rivers sun tabbatar da kama wata mata mai suna Gift bayan ta yanke mazakutar saurayinta a unguwar Diobu da ke Port Harcourt a jiya Alhamis.
Kotun Ebonyi ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga mutum hudu da suka hada baki suka kashe Chinonso Elom, wani matashi dan Ngbo, a ranar 5 ga Fabrairu, 2023.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da mutuwar mutum uku yayin da wasu 21 suka jikkata a cunkoson da ya faru a Bama da ke jihar Borno yayin rabon kudin tallafi.
Rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa tsohon matuƙin jirgin shugabannin ƙasa, Kyaftin Shehu Iyal ya rasu a ranar Alhamis bayan fama da jinya.
An tabbatar da mutuwar fitacciyar jaruma a masana'antar shirya fina finai ta Nollywood kuma mai rajin kare hakkin masu ƙima sosai a Najeriya, Monalisa Stephen.
Abun Bakin Ciki
Samu kari