Abun Bakin Ciki
An sace kansilan APC na Daudawa, Buhari Aliyu a hanyar Funtua, inda ake zargin wani mai baiwa ’yan bindiga bayani ne ya taimaka wajen yin garkuwa da shi.
Yayin da ake cigaba jimamin mutuwar Muhammdu Buhari, tsohon shugaban kungiyar kwadago, Ayuba Wabba ya bayyana babban rashi da aka yi bayan rasuwar dattijon.
Mutum 54 sun mutu cikin sa’o’i 24 a Pakistan sakamakon ruwan sama mai ƙarfi da ya haddasa ambaliya, rushewar gidaje, da katsewar wuta a yankunan da abin ya shafa.
Daya daga cikin hadiman Atiku Abubakar ya bayyana cewa an tono wasikar murabus dinsa daga jam’iyyar PDP mai adawa ba tare da izini ba a bainar jama’a.
Bayan rasuwar Sheikh Abdullahi Yankaba, Malam Lawan Abubakar Triumph ya bayyana jimaminsa kan rasuwar shehin cewa Sunnah ta yi babban rashi a Kano.
Diyar marigayi tsohon shugaban kasa, Hadiza Mohammed ta bayyana yadda suka ci N15 da aka rage musu bayan sayayya, amma Buhari ya kore su saboda rashin kai canji.
Goggo Ummahani da Yaya Jidde, iyalan gidan Sarkin Kano Sanusi I, sun rasu, inda Sarkin Kano Muhammad Sanusi II ya jagoranci sallar jana’izarsu a Kano.
Tsohon minista a Najeriya, Farfesa Isa Ali Pantami ya yaba da kyawawan halayen marigayi Muhammadu Buhari inda ya ce sun zauna da shi na tsawon shekaru 24.
Fatima Buhari ta isa Daura cikin kuka yayin shirin jana'izar mahaifinta, yayin da gawar tsohon shugaban ke kan hanya daga Landan zuwa Katsina don binne shi.
Abun Bakin Ciki
Samu kari