Hakeem Baba Ahmed: Muhimman Bangarori 2 da Shugaba Tinubu Ya Kunyata Yan Najeriya

Hakeem Baba Ahmed: Muhimman Bangarori 2 da Shugaba Tinubu Ya Kunyata Yan Najeriya

  • Hakeem Baba-Ahmed ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙara tsananta matsin tattalin arziki da matsalar tsaro,
  • Ya ce miliyoyin yara ba sa zuwa makaranta saboda rashin tsaro, yayin da tsadar rayuwa da haɗarin da ke tattare da hanyoyi ke ci gaba da shafar al’umma
  • Shugaban PRP ya yi gargaɗin cewa rashin gudanar da sahihin zaɓe a 2027 na iya barazana ga haɗin kan Najeriya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Shugaban PRP, Hakeem Baba-Ahmed, ya zargi gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da ƙara ta’azzara matsin tattalin arziki da rashin tsaro a Najeriya.

Ya bayyana bangarorin tattalin arziki da tsaro a matsayin wadanda Tinubu ya yi mummunan gazawa, wanda har yanzu yan Najeiya ba su amfana da tsare-tsaren da ya kawo na.

Hakeem Baba Ahmed.
Shugaban jam'iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba-Ahmed Hoto: Hakeem Baba-Ahmed
Source: Twitter

Ya bayyana hakan ne a ranar Talata yayin wata hira da aka yi da shi a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels Television.ninda ya soki yadda gwamnatin ta gudanar da mulki bayan shafe shekaru uku da rabi a kan karagar mulki.

Kara karanta wannan

Tinubu na da abin da zai fada wa yan Najeriya su zaɓe shi a 2027? Baba Ahmed ya yi magana

Bangarorin da Tinubu ya gaza

Baba-Ahmed ya ce miliyoyin yara ba sa iya zuwa makaranta saboda rashin tsaro, yayin da haɗarin da ke kan manyan hanyoyi da hauhawar farashin kayayyaki ke ci gaba da jefa ’yan Najeriya cikin wahala.

“Yaran da ke zaune a yankunan da ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane suka ƙwace ba sa iya zuwa makaranta kwata-kwata,” in ji shi.

Shugaban PRP ya kuma yi tambaya kan yadda gwamnati ta tafiyar da tattalin arzikin ƙasar, yana mai cewa alkaluman da hukumomi ke fitarwa ba sa nuna irin wahalhalun da ’yan Najeriya ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.

Ya kuma soki tafiyar da ayyukan gine-ginen hanyoyi a hankali, inda ya kawo babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna a matsayin misalin hanyar da masu ababen hawa ke ci gaba da fuskantar barazanar tsaro.

Baba-Ahmed ya ce ya kamata gwamnati ta kammala ƙarin ayyukan more rayuwa idan aka yi la’akari da kuɗaɗen shiga da take samu daga man fetur.

Kara karanta wannan

"Kai ne Masar," Atiku ya maida martani bayan Tinubu ya yi misali da tarihin Annabi Musa AS

Baba Hamed ya tabo zaɓen 2027

Baba-Ahmed ya bayyana ra’ayinsa kan zaɓen shugaban ƙasa na 2027, yana mai cewa sakamakon zaɓen zai dogara ne da sahihancin yadda aka gudanar da shi.

Ya yi gargaɗin cewa gudanar da zaɓen da aka yi maguɗi a cikinsa na iya jefa haɗin kan Najeriya cikin barazana, musamman idan masu kaɗa ƙuri’a suka yi imanin cewa an yi watsi da zaɓinsu.

Bola Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu yana jawabi da wasu jiga-jigai da suka kai masa ziyara a Aso Rock Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Ya ce gwamnati da hukumomin zaɓe dole ne su tabbatar da cewa ’yan ƙasar da ke yankunan da matsalar ’yan bindiga da garkuwa da mutane ta shafa sun sami damar shiga zaɓen.

PRP ta soki takaita kamfen Tinubu

Kun ji cewa shugaban jam’iyyar PRP na kasa, Hakeem Baba- Ahmed, ya bayyana Shugaba Bola Tinubu a matsayin wanda ya gaza.

Ya kuma yi zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ba shi da wani abu da zai gaya wa ’yan Najeriya da zai sa su sake yarda da shi a babban zaɓen 2027 da ke ƙaratowa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262