Abun Bakin Ciki
Bayan wata daya da rasuwar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari a birnin London da ke Birtaniya, ma’aikatan gidansa a garin Daura sun yi jimamin rasuwarsa.
Gwamna Dauda Lawal ya kai ziyarar ta’aziyya ga al’ummomin da ‘yan bindiga suka kai hari a Kauran Namoda, ya yi Allah wadai da kisan da ake cigaba da yi wa al'umma.
Rundunar ‘yan sanda a jihar Gombe ta sanar da kama matasa da masu laifuffuka da dama har da cafke wani Dagaci bisa zargin aukawa wata yarinya ‘yar shekara 12.
Zababbar kansilar Ibeju-Lekki, Oluwakemi Rufai, ta rasu bayan mako biyu da rantsar da ita, abin da ya jawo martani mai zafi daga al’umma da jam’iyyar APC.
Rigima ta barke tsakanin manyan yan bindiga bayan Kachalla Alti ya kashe hatsabibin dan bindiga Dankarami Usaini a kauyen Matsuki, Zamfara, bayan rikicin nuna iko.
Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi, an ce an sake kama bakwai daga cikin su, yayin da shugaban NCoS ya sha alwashin hukunta masu hannu a lamarin.
Sanatan kasar Colombia da ke da niyyar neman takarar shugaban lasar, Miguel Uribe Turbay ya mutu bayan shafe sama da watanni 2 yana jinyar harbin da aka masa.
Wasu ma'aurata, Abdulsalam da Zainab da mutane 3 sun rasa rayukansu sakamakon mummunan hatsarin motar da ya rutsa da su a titin Kurfi zuwa Katsina.
Rahotanni sun tabbatar da cewa wasu matasa yan daba dauke da makamai sun kai wa direban mota daga yankin Arewacin Najeriya hari a Kudu maso Gabashin kasar.
Abun Bakin Ciki
Samu kari