Abun Bakin Ciki
Yayin da ake shari'a kan wadanda ake zargi da kisan matafiya a Plateau, Babbar kotun Jihar Plateau ta yi zama kan karar da ake bayan kisan masu halartar biki.
Hukumomin tsaro a Amurka sun cafke wata mata a kasar da ta yi barazana ga Shugaba Donald Trump a kafar sadarwa ta intanet domin daukar fansar rasa rayuka.
An yi jana'izar marigayi Alhaji Ahmed Momohsanni Ododo, mahaifin gwamnan jihar Kogi wanda Allah ya yiwa rasuwa ranar Litinin, manyan mutane sun halarta a Okene.
A Anambra, jami’an Agunechemba sun ci zarafin Jennifer Elohor, wata ƴar NYSC, inda suka yi mata tsirara bayan sun lakada mata duka. Gwamnati ta ce an kama jami'an.
Bayan ta da jijiyoyin wuya kan ganin yan sanda a Kano suna taimakawa dan siyasa rabon kuɗi ga jama'a, rundunar ta tabbatar da ɗaukar matakin ladabtarwa kan jami’an.
Gwamnatin jihar Benuwai ta mika sakon ta'aziyya ga iyalan marigayi mai ba gwamna shawara kan harkokin hulda da jama'a da siyasa, Mary Yisa, wacce ta rasu.
Rahotanni daga jihar Borno sun tabbatar da tashin wani bam da yara yan gwangwan suka dauko a bayan gari, mutum biyu sun jikkata yayin wasu 4 suka raunata.
Mahaifin gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ahmed Usman Ododo ya riga mu gidan gaskiya yana da shekaru 83 a duniya, gwamnati ta roki Allah Ya sanya shi a Aljannah.
Rahotannin da muke samu sun tabbatar da cewa jihar Kebbi ta yi babban rashi bayan sanar da rasuwar Mai Martaba Sarkin Zuru da ke jihar a Arewa maso Yamma a Najeriya.
Abun Bakin Ciki
Samu kari