Abun Bakin Ciki
Ana cikin jimamin rasuwar fitacciyar jarumar Kannywood, Saratu Gidado da aka fi sani da Daso, an sanar da mutuwar wata jarumar Nollywood, Adejumoke Aderounmu.
An tafka babban rashi bayan mutuwar ɗan Majalisar dokokin jihar Kano, Haliliu Kundila da ke wakiltar mazabar Shanono/Bagwai bayan ya sha fama da jinya.
Allah ya karbi rayuwar babban manaja a hukumar kula da hanyoyin ruwa (NIWA), Dardau Jibril a yau Juma'a 5 ga watan Afrilu bayan ya gama jagorantar sallar asuba.
Babbar Kotun Tarayya da ke Legas ta sanya 9 ga watan Afrilu a matsayin ranar yanke hukunci kan ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky.
A safiyar yau Juma'a ne mahaifiyar mataimakin gwamnan jihar Kwara, Mama Ena Maud Alabi ta rigamu gidan gaskiya, Gwamna AbdulRazaq ya mika sakon ta'aziyya.
Mutane sun shiga fargaba bayan wata babbar mota ta kauce hanya tare da kutsawa cikin masallaci bayan idar sallar tahajjud a jihar Neja da ke Arewacin Najeriya.
Hukumar EFCC ya tabbatar da kame fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky a daren jiya Laraba 3 ga watan Afrilu a jihar Legas.
An tafka babban rashi a masana'antar Nollywood bayan rasuwar shararren furodusa kuma darektan fina-finai, Frank Ogho Vaughan wanda ya ba da gudunmawa sosai.
An shiga cikin firgici yayin da shugaban jam'iyyar LP, Julius Abure ya sha da kyar bayan gobara ta kama gidansa sa ke birnin Abuja da safiyar yau Laraba.
Abun Bakin Ciki
Samu kari