Jami'an Gwamnatin Kano Sun Yi Tattaki zuwa Jihar Ribas, Sun Kamo Wani Mutumi da Ake Zargi
- Rundunar yaƙi shaye-shayen miyagun ƙwayoyi da safararsu ta Kano ta tafi har jihar Rivers, ta kama wani da ake zargi da jagorantar ƙungiyar ’yan daba
- Shugaban rundunar, Muhuyi Magaji, ya ce an dawo da wanda ake zargin Kano domin gurfanar da shi a gaban kotu
- Ana zargin Malam Keya da jagorantar tashe-tashen hankula tsakanin ’yan daba da suka yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kano – Rundunar haɗin gwiwa ta yaƙi miyagun ƙwayoyi da safararsu ta jihar Kano ta yi tattaki zuwa jihar Ribas da ke Kudancin Najeriya ta kamo wani ɗan daba.
Rundunar ta kama wani da ake zargi da jagorantar ƙungiyar ’yan daba, Ishaq Lawan Ibrahim, wanda aka fi sani da Malam Keya, a Fatakwal da ke jihar Rivers.

Source: Facebook
Premium Times ta rahoti cewa shugaban rundunar, Muhuyi Magaji Rimingado ne ya sanar da kamen a ranar Alhamis, inda ya ce an dawo da wanda ake zargin Kano domin fuskantar shari’a.
A cewarsa, wanda ake zargin ya tsere daga jihar Kano ne bayan an ayyana shi a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo bisa zargin hannu a rikicin ƙungiyoyin ’yan daba da ya yi sanadin mutuwar mutane da dama.
Yadda aka kama Malam Keya
Magaji ya ce Malam Keya, mai shekaru 27, ɗan unguwar Yelwa ne da ke ƙaramar hukumar Dala a jihar Kano.
Ana zargin sa da taka muhimmiyar rawa wajen haddasa rikice-rikicen ƙungiyoyin ’yan daba da suka kawo cikas ga zaman lafiya a wasu sassan jihar.
A cewarsa, ana zargin matashin da jagorantar ƙungiyar ’yan daban tare da ɗaukar nauyin ayyukan tashin hankalin da suka jawo asarar rayuka da kuma tsoratar da mazauna ƙaramar hukumar Dala.
Ya bayyana cewa wanda ake zargin ya tsere daga Kano ne bayan rundunar ta ƙara tsaurara matakan tsaro a yankunan da rikicin ’yan daba ya shafa, ciki har da Jakara, Madigawa, Yalwa, Sanka, Kul Kul, Dogon Nama, Kuka Bulukiya, Dala, Shatsari da Dandalin Turawa.

Kara karanta wannan
Sojoji sun ceto mutane 70, sun kama ƙasurgumin ɗan bindiga da ya addabi mutane a Arewa
Magaji ya ce jami’an rundunar sun bi sahun wanda ake zargin bayan samun sahihan bayanan sirri, inda suka gano shi a Fatakwal tare da kama shi a wani samame da shugaban sashen ayyuka na rundunar, CSP Bashir Gwadabe, ya jagoranta.
Ya ƙara da cewa an riga an dawo da shi Kano domin fuskantar shari’a.
Ba za a bar masu ɗaukar nauyi ba
Magaji ya yi gargaɗin cewa rundunar ba za ta sassauta ƙoƙarinta na kama mutanen da ke ɗaukar nauyin tashin hankali ba, ko da sun tsere zuwa wasu jihohi.
Ya ce:
“Masu ɗaukar nauyin tashin hankali su sani cewa babu nisan da za su je ko wurin ɓuya da zai kare su. Wannan kamen mafari ne kawai. Ba za mu huta ba har sai an dawo da cikakken zaman lafiya.”
Asali: Legit.ng
