Abuja
Shugabanni sun hallara a Abuja don kaddamar da littafin IBB. Obasanjo zai jagoranci taron, Tinubu babban bako ne, yayin da Osinbajo zai nazarci littafin.
Rahotanni sun tabbatar da cewa rikici ya barke a majalisar dattawa yayin da aka matsar da kujerar Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan, amma ta ki amincewa.
Jarumar Kannywood, Rahama Sadau ta gana da ministan tsaro, Bello Matawalle da ministan yada labarai, Mohammed Idris a kan shirin baje kolin al'adun Arewa a Abuja.
Masana sun yi magana kan dalilan da Naira ke kara daraja idan aka kwatanta da dala inda su ke ganin hakan na da alaƙa da matakan da bankin CBN ke ɗauka.
Yayin da ake kokawa kan yawan haduran tankokin mai da ake samu, Hukumar NMDPRA ta haramta amfani da tankokin mai masu daukar lita 60,000 a hanyoyin Najeriya.
Kungiyar 'yan shi'a ta kasa (IMN) ta zargi jami'an tsaron Najeriya da shiga hakkinta ta hanyar hana membobinta gudanar da taro cikin lumana, bayan doka ta basu dama.
Wani matashi ya sassara abokinsa da adda yayin da ya gayyace shi gida cin abinci. Matashin ya sara shi a kayi da jikinsa. Yan sanda sun kama matashin a Abuja.
‘Yan bindiga sun kashe wasu matasa biyu a Gwargwada, Abuja, saboda jinkirin fansa. Sun sako wasu mutum uku bayan karɓar N3m. Har yanzu ba a samu gawarwakin ba.
Mai kudin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana kalubalen da ya fuskanta yayin gina matatar mai da ke Legas. Ya ce da ya gaza karasa aikin da ya samu karayar arziki.
Abuja
Samu kari