Abuja
Tsohon kakakin Majalisar Wakilai a Najeriya, Yakubu Dogara ya sanar da rasuwar mahaifiyarsa, Mama Saratu Yakubu Tukur ta na da shekaru 103 a duniya.
Wasu da ba a san ko su waye ba sun kai harin ramuwar gayya a wata rugar Fulani a garin Kpache, karamar hukumar Abaja da ke birnin Abuja inda suka kashe mutum 2.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta saka ranar 3 ga watan Faburairun 2024 don sake zabe saboda cike gurbin kujerun da suke babu kowa a fadin kasar.
Mako daya bayan sallamar daraktoci a ma'aikatar harkokin jiragen sama, Shugaba Tinubu ya sake nada sabbin daraktoci 46 a hukumomi daban-daban a ma'aikatar.
Nyesom Wike ya ce mutanen da ke zaune a yankin Nuwalege su bar gidajensu domin za a rusa su. Rundunar sojojin sama su ka bukaci a tashi unguwar Nuwalege.
Tsohon Ministan wutar lantarki a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo, Olu Ogunloye ya shiga hannun hukumar EFCC bayan nemanshi da ake ruwa a jallo a makon jiya.
Shugaba Bola Tinubu ya shiga ganawar gaggawa kuma ta sirri da Gwamna Siminalayi Fubara na jihar Rivers da kuma tsohon Gwamna Peter Odili a fadarsa da ke Abuja.
An shiga tashin hankali yayin da zanga-zanga ta nemi zama tashin tashina a Abuja, tuni dai jami'an tsaro suka damƙe mutane 19 daga cikin masu kunnen ƙashin.
Hukumar kula da kwarewar malamai ta kasa, TRCN ta tabbatar da cewa akalla malamai dubu uku su ka fadi jarabawar hukumar yayin da dubu 10 su ka tsallake.
Abuja
Samu kari