Abuja
A labarin nan, za a ji cewa tsohon hadimin Shugaban Kasa, Reno Omokri ya ja tawaga domin tabbatar da tsaron da aka samu a hanyar Abuja zuwa Kaduna.
Hukumar NiMet ta gargadi mazauna yankunan bakin teku da su shirya yayin da ta yi hasashen cewa ruwan sama mai yawa zai sauka a Kano, Neja da wasu jihohin Arewa 14.
Yayin da PDP ta tura tikitin takarar shugaban kasa zuwa Kudancin Najeriya, Gwamna Bala Mohammed ya ce jam'iyyar ta koyi darasi daga kuskuren APC a 2023.
Gwamnatin Tarayya ta karrama daliba daga jihar Yobe, Nafisa Abdullahi wacce ta lashe gasar Turanci ta duniya da aka yi a London, inda ta ba ta kyautar N200,000.
Shugaban kamfanin man fetur na kasa (NNPCL), Bayo Ojulari, ya ce wasu kusoshi a fannin fetur da gas na barazana ga rayuwarsa saboda yana shirin gyara matatun mai.
Sanata Dino Melaye zai gurfana gaban kotu bisa tuhumarsa da ake yi da guje wa biyan harajin kuɗin shiga da ya kai N509.6m. An ce ya ki biyan kudin a 2023 da 2024.
Shugaban hukumar sufurin jiragen kasa ta Najeriya, Opeifa ya ce zai yi duk mai yiwuwa wajen hana aake faruwar hatsarin jirgin kasa a layin dogon Abuja zuwa Kaduna.
Limamin Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya yi Allah wadai da kama shugaban Falasdinawa, Abu Ramzy Ibrahim a Abuja. Ya ce cin fuska ne ga Musulman Najeriya.
Bayan faruwar iftila'i a Najeriya, Hukumar jiragen kasa ta Najeriya (NRC) ta dakatar da zirga-zirgar jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna bayan hatsari.
Abuja
Samu kari