Abuja
Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta dakile masu shirin gudanar da zanga-zanga a gobe Alhamis 1 ga watan Agustan 2024 inda ta ce a filin wasa kawai za su tsaya.
Karamin Ministan karafa a Najeriya, Uba Maigari ya roki 'yan jihar Taraba alfarma da su guji fita kan tituna domin gudanar da zanga-zanga da ake shirin yi.
Majalisar dattawan Najeriya ta bukaci 'yan Najeriya da su kara ba shugaban kasa Bola Tinubu lokaci. Godswill Akpabio ne ya yi wannan rokon a Abuja.
Shugaban majalisar dattawan Najeria, Sanata Godswill Akpabio ya hadu da fushin matasan Najeriya bayan ya yi magana da ta jawo cece ku ce a kan zanga zanga.
Rahotanni sun nuna cewa ana ci gaba da shirye-shiryen fara gudanar da zanga-zanga a fadin Najeriya. An bayyana jerin wuraren da za a gudanar da ita.
'Yan sanda sun samu nasarar cafke wata matar aure da ake zargin ta kashe mijinta bayan sun samu hatsaniya kuma ta yi kokarin guduwa da kayansa bayan kone gawarsa.
Matasa a Najeriya na ci gaba da shirye-shiryen fitowa domin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan. Zanga-zangar za a yi ta ne saboda tsadar rayuwa da talauci.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa masu zanga-zanga su guji zuwa gidajen gyaran hali da tarbiyya domin hana kokarin ba wa masu laifi damar tserewa da daga gidan.
Tsohon shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Uche Secondus ya ce shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ba zai iya hana zanga-zanga ba saboda shi ma ya ci moriyarta.
Abuja
Samu kari