Abuja
Rahotanni sun bayyana cewa dakarun sojojin Najeriya sun kafa shingen binciken ababen hawa a titin Keffi-Abuja sa'o'i 24 gabannin fara zanga-zangar tsadar rayuwa.
Kungiyoyin matasan Najeriya sun yi martani ga Nyesom Wike kan amfani da dandalin Eagle Square domin gudanar da zanga zanga. Damilare Adenola ne ya yi martanin.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Ezenwo Wike ya fara tattaunawa da matasan birnin domin kakkabe ra'ayinsu na shiga zanga-zanga saboda illarsa.
Fadar shugaban kasa ta fito ta musanta batun wani jawabi da ake cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya yi inda ya dauki matakan tsuke aljihun gwamnati.
Ministan Abuja, Nyesom Wike ya zargi wasu 'yan siyasa da ba su yi nasara a zabe da shirya wannan zanga-zanga domin kifar da gwamnatin Tinubu a kasar.
Hukumar matasa masu yiwa kasa hidima ta NYSC ta yi gargadi kan shiga zanga-zanga musamman masu bautar kasa inda ta ce haramun ne su shiga lamarin.
Shugaban jam'iyyar APC, Abdullahi Ganduje ya kira wata ganawa da shugabannin APC a jihohi 36 a kasar yayin da ake shirin shiga zanga-zanga na halin kunci.
'Yan majalisar wakilai daga yankin Arewa maso Yamma sun yi kira ga mutanen yankin da su hakura da fitowa zanga-zangar da aka shirya gudanarwa a fadin kasar nan.
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima, ya bukaci 'yan Najeriya da su hakura da fitowa kan tituna domin gudanar da zanga-zanga a fadin kasar nan.
Abuja
Samu kari