Abuja
Babbar kotun tarayya mai zama a babban birnin tarayya Abuja ta kori karar da wasu ƴan Najeriya suka nemi a dakatar da masu zanga-zanga daga sake fitowa.
Rundunar 'yan sandan Kano ta bayyana cewa ta damke akalla mutane 873 bisa zargin karya doka kwanakin da aka gudanar da zanga zanga a jihar, an kai wasu Abuja.
Gwamnatin Tarayya ta dakatar da wani bangare na aikin babbar hanyar Kano zuwa Maiduguri saboda sakaci na 'yan kwangila da bata lokaci a aikin na tsawon lokaci.
Kotun Koli ta umarci ba kansiloli da shugabannin kananan hukumomi a Najeriya wa'adin shekaru hudu kamar yadda gwamnonin jihohi ke yi a tsarin mulki.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta hannun kakakinta, Muyiwa Adejobi, ta bayyana cewa ba za ta iya cafke dukkanin masu aikata laifuka ba a lokaci daya.
Rahotanni sun bayyaɓa cewa tun da duku-duku matasa masu zanga zanga sun fito kan tituna a babban birnin tarayya Abuja duk da tulin jami'an tsaro da aka jibge.
Rundunar 'yan sandan Najeriya ta fito ta yi karin haske kan dalilin jami'anta na kai samame a hedkwatar kungiyar kwadago ta kasa da ke babban birnin tarayya Abuja.
Mataimakin shugaban kasar, Kashim Shettima ya bayyana shirye-shiryen Bola Tinubu kan matasa inda sha alwashin cigaba da tafiya da su a wannan gwamnati.
Kungiyar Arewa Young Leaders Forum (AYLF) ta bukaci gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed da ya janye kalamansa tare da neman afuwar Shugaba Tinubu.
Abuja
Samu kari