Bola Tinubu
A wannan labarin, za ku ji tsohon dan takarar shugaban kasa a zaben 2023, Felix Osakwe ya shawarci shugaba Bola Ahmed Tinubu ya ajiye mukamin Ministan man fetur.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya ce nasarar APC a zaben Edo ya nuna akwai alamar talakawa sun amince da salon mulkin Bola Tinubu.
Jam'iyyar APC reshen Zamfara ta roki Bola Tinubu ya sanya dokar ta baci a jihar saboda matsalar ta'addanci inda ta zargi Gwamna Dauda Lawal da kawo cikas.
Sanata Kofowola Bucknor-Akerele wacce ta rike muƙamin mataimakiyar Bola Tinubu a jihar Lagos ta koka kan irin halin shugaban na rashin karbar shawara.
Tsohon shugaban NESG, Kyari Bukar ya bayyana cewa Bola Tinubu ya biyo hanya mai gargada wajen tuge tallafin man fetue shiyasa aka shiga ƙangin wahala.
Daga dawowar shugaban kasa ya fuskanci matsalar ambaliyar ruwa, kudin fetur, zaben Edo da ASUU. Daga cikin bukatun da ASUU ke da su akwai biyan albashin malamanta.
Shugaba Bola Tinubu ya fadi dalilin zuwansa fadar shugaban kasar Najeriya inda ya ce ko kusa ba maganar kwasar kudi ba ne ya kai shi 'Aso Rock' a Abuja.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan halin kunci da ake ciki a kasar inda ya jingina laifin ga matakan da aka dauka a baya.
Kwamitin tsarawa da gyara albashin ma'aikata (NSIWC) ya tabbatar da cewa za a tabbatar da fara biyan mafi ƙarancin albashin N70,000 tun daga watan Yulin 2024.
Bola Tinubu
Samu kari