Bola Tinubu
A ranar Juma'a Bola Ahmed Tinubu ya cigaba da yin nadin mukamai. An amince da nadin mukamai a hukumar da aka kawo domin cigaban Kudu maso gabas a Najeriya.
An nada shugabannin wasu hukumomin gwamnatin tarayya. Mai taimakawa shugaban kasa wajen yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar da sanarwa.
Yayin da ake ta yada rade-radin za a kafa sansanin sojojin Faransa a Najeriya, rundunar tsaro ta musanta labarin, ta fadi yarjejeniyar da Bola Tinubu ya yi.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya aika saƙon ta'aziyya ga iyalan Marigayi Sheikh Muyideen Bello, wanda Allah ya yi ma rasuwa ranar Juma'a a Ibadan.
Najeriya da Faransa sun kulla yarjejeniyar hako ma'adanai. Hakan ya jawo shakku ga yan Najeriya domin jin tsoron Faransa za ta iya jawo matsalar tsaro a Arewa.
Matasan Arewa sun ce ba dai-dai ba ne sukar Barau I Jibrin. Mataimakin shugaban majalisa ya na shan suka a kan goyon bayan kudirin harajin Bola Tinubu.
Shugaba Bola Tinubu ya jawo aikin sama da Naira triliyan 4 a masarautar Borgu da ta ba shi Jagaba. Kamfanin Brazil zai zuba hannub jarin $2.1bn a Borgu.
Gwamnan Imo, Hope Uzodinma ya yi kira ga ƴan Najeriya kada su zauna a duhu suna sukar abin da ba su da ilimi a kansa, ya buƙaci mutane su karanta kudirin haraji.
"Dole ne gwamnonin Arewa su farka." Tsohon dan takarar shugaban kasa ya ce kudirin harajin Tinubu ya bankado matsalolin Arewa, kuma ya dace a magance su.
Bola Tinubu
Samu kari