Bola Tinubu
Yayin da tarun matsaloli suka yi yawa a Arewa, Sheikh Murtala Bello Asada ya ce zai yi wahala Tinubu ya tsallake zabe a 2027 ya danganta hakan da nakasa yankin.
Yayin da ake zargin neman ta da husuma, Gwamna Ademola Adeleke ya zargi tsohon gwamna Adegboyega Oyetola da shirin tayar da zaune tsaye a Jihar Osun.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya taya tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai murnar cika shekara a duniya. Tinubu ya yaba da hazakarsa.
Shugaban APC, Abdullahi Ganduje, ya ce Arewa ta hakura da takarar 2027, amma wasu manyan yankin sun ce wannan matsayi barazana ce ga tsarin dimokuradiyya.
Siyasar Arewa ta dauki sabon salo yayin da aka rabu kan yiwuwar sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027, yayin da wasu ke goyon bayansa, wasu kuma na adawa.
Gwamnatin tarayya ta nemi sabon bashin dala miliyan 300 daga Bankin Duniya don inganta kiwon lafiya, NCDC ce za ta aiwatar da shirin a shekarar 2026.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir Lawal ya gargadi Bola Tinubu kan zaben 2027 inda ya ce dole ya sasanta da Arewacin kasar domin samun nasara.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bukaci gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya shiga cikin batun takaddamar filin jami'ar BUK domin kawo karshen matsalar.
Tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, ya caccaki gwamnatin jam'iyyar APC. Ya yi wa 'yan siyasa wankin babban bargo kan sauya jam'iyya.
Bola Tinubu
Samu kari