Yan ta'adda
Shugaban sojojin kasan Najeriya, Laftanal Janar Olufemi Oluyede ya ce suna bin Bello Turji sau da kafa domin kawar da shi. Ana bin diddin dan ta'addar a Zamfara.
Kwamandan sojin Amurka a Afrika, Janar James Hecker ya ce za su dawo kai farmaki kan Boko Haram da saurann 'yan ta'adda a Afrika domin samar da tsaro.
Rundunar 'yan sandan Zamfara ta tabbatar da cewa wani abin fashewa ya jawo gobara a wata kasuwa dake jihar, har ta yi sanadiyyar konewar mutane da dama.
Wani matashi ya sassara abokinsa da adda yayin da ya gayyace shi gida cin abinci. Matashin ya sara shi a kayi da jikinsa. Yan sanda sun kama matashin a Abuja.
Gwamnatin Donald Trump za ta binciki tallafawa Boko Haram da kidin USAID bayan Sanatan Amurka ya bankado bayanai. Amurka ta yi Allah wadai da Boko Haram.
Rundunar 'yan sandan Adamawa ta tabbatar wa legit cewa jami'anta su na kokarin ceto mutanen da miyagun 'yan ta'adda su ka sace bayan kai mummunan hari a jihar.
Wasu da ake zargi da kisan dan majalisar Anambra sun tsere daga hannun ‘yan sanda. Kwamishinan 'yan sanda ya tura jami’ai don kamo su tare da hukunta masu sakaci.
Wasu rahotanni sun ce ana hasashen batan tsohon shugaban karamar hukumar Kalgo a jihar Kebbi, Umar Namashaya Diggi bayan wani mummunan harin yan bindiga.
Hatsabibin dan fashi a jihar Zamfara, Gwaska Dankarami, na shirin mika wuya bayan arangama da Sani Dangote inda wasu suka ce ana nemansa ruwa a jallo.
Yan ta'adda
Samu kari